Episode's summary
A tsakiyar wannan makon ne dai kotun sauraron ƙararrakin wasanni ta Duniya CAS ta yanke hukuncin maida wa Senegal kofin gasar ƙasashen Afrika ta AFCON ta shekarar 2025 da hukumar CAF ta ƙwace daga hannunta ta kuma miƙa wa Morocco. Hukuncin dai ya kawo ƙarshen taƙaddama tsakanin ƙasashen biyu kan wasan ƙarshen da suka fafata a ranar 18 ga Janairun wannan shekara ta 2026.
A tsakiyar wannan makon ne dai kotun sauraron ƙararrakin wasanni ta Duniya CAS ta yanke hukuncin maida wa Senegal kofin gasar ƙasashen Afrika ta AFCON ta shekarar 2025 da hukumar CAF ta ƙwace daga hannunta ta kuma miƙa wa Morocco. Hukuncin dai ya kawo ƙarshen taƙaddama tsakanin ƙasashen biyu kan wasan ƙarshen da suka fafata a ranar 18 ga Janairun wannan shekara ta 2026.
Episodes
Kotun sauraron ƙararrakin wasanni TAS ta yanke hukuncin maida wa Senegal kofin ta AFCON
ListenedA tsakiyar wannan makon ne dai kotun sauraron ƙararrakin wasanni ta Duniya CAS ta yanke hukuncin maida wa Senegal kofin gasar ƙasashen Afrika ta AFCON ta shekarar 2025 da hukumar CAF ta ƙwace daga hannunta ta kuma miƙa wa Morocco. Hukuncin dai ya kawo ƙarshen taƙaddama tsakanin ƙasashen biyu kan wasan ƙarshen da suka fafata a ranar 18 ga Janairun wannan shekara ta 2026.
Rawar da tawagogin Najeriya suka taka a wasannin neman shiga AFCON da Olympic
ListenedShirin a wannan makon zayyi duba ne kan wasanni sharen fagen zuwa gasar lashe kofin nahiyar Afrka ta AFCON da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi tsakaninta da Tanzania, bayaga wanda itama tawagar ƴan ƙasa da shekaru 23 da aka fi sani da Olympics Eagles ta yi da takwararta ta DRC. Bayaga tawagar Super Eagles, ita dai ƙanwarta ta ƴan ƙasa da shekaru 23 wato Olympics Eagles, ta buga nata wasannin neman gurbin tsakaninta da takwararta ta DRC, inda wasan farko tasha kashi da ci 2 da nema, amma a wasa na biyu da ya gudana a filin wasa na Remon Stars da ke garin Ikenne a jihar Ogun, Najeriyar ce ta maida biki ta hanyar lallasa DRC da ci 4 da nema, wani al’amari da ya bata damar tsallakawa zagaye na gaba inda za su ƙara da Zambia, a wasannin neman gurbin zuwa gasar AFCON ta wannan mataki, haɗi da neman gurbin zuwa gasar Olympics da za a yi a shekarar 2028.
Tagomashin da tawagar Flamingos ta samu bayan lashe kofin duniya
ListenedShirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya maida hankali ne kan nasarar lashe kofin duniya na mata ƴan ƙasa da shekaru 17 da tawagar Flamingos ta Najeriya ta yi, bayan da ta lallasa takwararta ta Japan a wasan ƙarshe da ci 2-1. Tuni dai shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje ƴan matan da kyautar naira miliyan Ɗari-ɗari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............
Bamuji ɗaɗin irin rabuwar da aka yi tsakanin Ronaldo da Portugal ba - Ra'ayoyi
ListenedShirin na duniyar wasanni a wannan lokaci yayi duba ne game da bankwana da tawagar Portugal da Ronaldo yayi. A cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa, lamarin da ke kawo ƙarshen shekaru fiye da 20 da ya shafe yana wakiltar ƙasar shi a matakin ƙwallon ƙafar duniya. Cikin saƙon na Ronaldo, ya ce bayan nutsuwa cikin tsananki ya fahimci cewa lokaci ya yi da zai kawo ƙarshen wakiltar ƙasar shi kodayake ya ce Portugal za ta ci gaba da kasancewa a zuciyar shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............
Sharhi akan kyautar Ballon d'Or ta 2026 wadda Harry Kane ya lashe
ListenedShirin 'Duniyar Wasanni' tare da Khamis Saleh zai maida hankali ne kan kyautar Ballon d’Or da aka bayar a ranar Litinin ɗin data gabata. Kyaftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ya lashe kyautar a bana, inda ya zamo ɗan wasan ƙasar na farko daya lashe ta cikin shekaru 25, wato tun bayan Michael Owen a shekarar 2001. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin...........