Episode's summary
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta sanar da ranar da za ta gudanar da atisayen gwaji na tantance masu zaɓe da kuma amfani da na’urorin BVAS, domin tabbatar da shirye-shiryenta kafin babban zaɓe. Sai dai yayin da ake ƙoƙarin inganta tsarin zaɓe, wani rahoto ya nuna cewa an samu aukuwar hare-haren siyasa 124 cikin watanni huɗu, waɗanda suka yi sanadin mutuwar mutane 22. A wani labarin kuma, Shugaba Bola Tinubu ya sake yin alƙawarin ceto yaran makarantar da aka sace a jihar Borno, watanni shida bayan sace. Wannan alƙawari ya janyo martani daga masu sharhi kan harkokin siyasa. Wannan da ma wasu batutuwan na ƙunshe a cikin shirin ‘Dandalin Siyasa tare da Michael Kuduson. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Episodes
An samu hare-haren siyasa 124 a watanni 4 a Najeriya makwanni 6 gabanin zaɓen 2027
ListenedYayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta sanar da ranar da za ta gudanar da atisayen gwaji na tantance masu zaɓe da kuma amfani da na’urorin BVAS, domin tabbatar da shirye-shiryenta kafin babban zaɓe. Sai dai yayin da ake ƙoƙarin inganta tsarin zaɓe, wani rahoto ya nuna cewa an samu aukuwar hare-haren siyasa 124 cikin watanni huɗu, waɗanda suka yi sanadin mutuwar mutane 22. A wani labarin kuma, Shugaba Bola Tinubu ya sake yin alƙawarin ceto yaran makarantar da aka sace a jihar Borno, watanni shida bayan sace. Wannan alƙawari ya janyo martani daga masu sharhi kan harkokin siyasa. Wannan da ma wasu batutuwan na ƙunshe a cikin shirin ‘Dandalin Siyasa tare da Michael Kuduson. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Dandalin siyasa,shirin da ke kawo muku irin wainar da ake toyawa a fagen siyasa
ListenedA wannan makon, majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da kudirin kafa ƴansandan jihohi. Sai dai yayin da ake murnar wannan mataki, wasu na nuna fargabar cewa gwamnonin jihohi za su iya amfani da wannan runduna wajen musgunawa ƴan adawa.
INEC a Najeriya ta cire sunayen bogi, sama da milyan 1 da dubu 600
ListenedA cikin shirin dandalin siyasa na yau, za mu ji cewa a yayin da ake cigaba da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta bayyana cewa ta cire sunayen bogi, sama da miliyan 1 da dubu 600 daga rajistar masu zaɓe, bayan gano kura-kurai da wasu jami’anta suka tafka-------------
Ɗaukaka ƙara daga ADC za ta dakatar da hukuncin kotu kan Atiku da jam'iyyar?
ListenedA cikin shirin namu na yau, za mu ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark, tare da dukkan matakan da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a zaɓen 2027. Za mu ji martanin Nafiu Bala Gombe, wanda ya shigar da ƙarar, da kuma martanin tawagar Atiku.
ADC ta magantu kan ikirarin da APC ta yi cewa Tinubu ya nada goyan bayan Arewa
ListenedA cikin shirinmu na yau tare da Michael Kuduson za mu yi waiwaye akan babban gangamin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a Kaduna,, inda shugabannin jam’iyyar suka yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da goyon bayan Arewa. Za mu kuma ji martanin jam’iyyar ADC kan wannan ikirari, musamman batun cewa sama da mutum miliyan ɗaya ne suka halarci gangamin. Latsa alamar sauti don sauraron karin bayani.....