Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

00:00
00:00

Episode's summary

'Al’adunmu Na Gado' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya sake yin tattaki ne zuwa garin Ingal da ke Yankin Agadez a Jamhuriyyar Nijar, inda aka gudanar da bikin ala’adu na ƙasa baki ɗaya da ke haɗa makiyaya daga ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee'. An dai saba gudanar da bikin makiyayan ne a kowane makon farko na cikin watan Oktoba, da zummar ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya don zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu.

Episodes

401-

Bikin al'adun makiyaya na ƙasa a Jamhuriyar Nijar

'Al’adunmu Na Gado' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya sake yin tattaki ne zuwa garin Ingal da ke Yankin Agadez a Jamhuriyyar Nijar, inda aka gudanar da bikin ala’adu na ƙasa baki ɗaya da ke haɗa makiyaya daga ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee'. An dai saba gudanar da bikin makiyayan ne a kowane makon farko na cikin watan Oktoba, da zummar ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya don zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin ƙabilu.

13 Oct 2026
400-

Mahukuntan Nijar sun karrama fitaccen mawaƙin gargajiya Mamman Gawo Filinge

Da yake mawaƙan gargajiya na da matuƙar tasiri a ƙasar Hausa, mahukunta sun karrama fitaccen mawaƙin Nijar, Marigayi Alhaji Mamman Gawo Filinge, inda aka raɗawa wani titi sunansa. Mawaƙin ya taka gagarumar rawa sakamakon waƙokinsa na siyasa da na gargajiya, da noma da kuma zamantakewa, lokacin da ya yi zamaninsa a shekarun 1960 zuwa 1980. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

06 Oct 2026
399-

Jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin ranar Hausa ta bana a ƙasar

Shirin Al’adumu na gado a wannan makon ya sake waiwayar baukukuwan ranar Hausa ne ta Duniya, ranar da babban taronta ke gudana a dukkanin ranakun 26 ga watan Agusta duk shekara, to amma kasancewar bikin ya samu karɓuwa a gwamman ƙasashe ya sa bayan babban taron ake gudanar da wasu ƙarin bukukuwan ranar hausar ta Duniya a ƙasashe daban daban, ciki har da Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da bikin zagayowar ranar hausar ta Duniya a ranar 8 ga watan Satumban da muke. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Nura Ado Sulaiman.

15 Sep 2026
398-

Muhawara kan banbance tsakanin ƙabilun Hausawa da kuma Fulani a Najeriya

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan zamantakewa da auratayyar ƙabilun Hausawa da Fulani, ƙabilu 2 da suka juye zuwa Hausa Fulani bayan zaman tare na tsawon shekaru musamman a Najeriya. A baya-bayan nan muhawara ta fara zafi kan buƙatar banbance ƙabilun biyu zuwa Hausa daban da kuma Fulani zalla, lamarin da ya ci karo da fahimtar wasu daga cikin masana a ɓangaren al'adu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

08 Sep 2026
397-

Batutuwan da bikin 'Ranar Hausa ta Duniya' zai mayar da hankali kai a bana

Shirin Ala'adunmu na gado a wannan mako ya mayar da hankali ne kan 'Ranar Hausa ta Duniya' 'lokaci na musamman da ake amfani da shi wajen tunatar da muhimmancin harshen Hausa da kuma Al’adun Hausawa. Ku danna alamar sautin da ke sama domin sauraron cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa...........

25 Aug 2026